5 Oktoba 2020 - 11:49
​Zarif Ya Gana Da Sabon Sarkin Kuwaiti A Ziyarar Da Ya Kai A Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya kai ziyara kasar Kuwait a yau Lahadi, inda ya gana da sabon sarki, Sheikh Awaf al-Ahmad al-Sabah.

ABNA24 : Tun da fari, ministan harkokin wajen na Iran ya sami tarbar ministan tsaron kasar Kuwait na wucin gadi, Dr. Ahamd Nassir al-Mohammad al-Sabah, kuma ministan harkokin waje.

Muhammad Jawad Zarif ya mika sakon ta’aziyyar shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani da kuma al’ummar Iran ga sabon sarkin na Kuwaiti bisa rasuwar Sheikh Saban al-Ahamd al-Jabir al-Sabah.

Bugu da kari ya kuma taya sabon sarkin murna, tare da fatan cewa alaka a tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da bunkasa.

342/